Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa ta bayar da diyyar naira miliyan 287 ga mutane 74 da aka kashe a zanga-zangar EndSars

0 130

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa a jiya ta bayar da diyyar naira miliyan 287 ga mutane 74 da suka ci gajiyar diyyar ta’asar ‘yansanda.

Kwamitin yana binciken take hakkin dan adam daga rusasshiyar tawagar ‘yansanda ta SARS, da sauran sassan ‘yan sanda.

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin ne a watan Nuwambar 2020 biyo bayan zanga-zangar ENDSARS da aka yi sakamakon zarge-zargen cin zarafin da ‘yan sanda ke yi a fadin kasarnan.

An bayar da kason farko na diyyar ta naira miliyan 146 a ranar 23 ga watan Disambar 2021 ga mutane 26.

Da take jawabi, shugabar hukumar kula da kare hakkin bil’adama ta kasa, Dr Salamatu Suleiman, ta taya masu shigar da kara murnar amincewa da tsarin kare hakkin bil’adama a Najeriya.

Kazalika, Sakataren zartarwa na Hukumar, Anthony Ojukwu, ya bayyana bikin a matsayin muhimmin abu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: