Hukumar Kare Muhalli Ta Jihar Jigawa Ta Haramta Sare Itatuwa A Fadin Jihar

0 65

Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa ta haramta sare itatuwa a fadin jiharnan, da duk wani aiki da ya shafi masu yin gawayi ba tare da amincewar hukumar ba kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Manajan Daraktan hukumar Injiniya Lawan Ahmed.

A cewar sanarwar, wadannan bishiyoyi suna tallafawa rayuwa kuma suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar tattalin arziki da zamantakewa.

Ya kara da cewa sakamakon sare wadannan bishiyoyi yana da yawa, wanda ya samo asali daga raguwar rabe-raben halittu da asarar muhalli, sauyin yanayi, kwararowar hamada, asarar ruwa da albarkatun kasa, sakamakon tunani da zamantakewar al’umma.

Hukumar ta bukaci goyon bayan jama’a a dukknin ayyukanta na kare muhalli daga lalacewa, kamar yadda doka ta umarce ta da ta hana, tare dakatar da duk wasu ayyukan da ba su dace ba da ke iya gurbata muhalli da nufin kare muhalli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: