Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tayi nasarar ceto rayukan mutane 60 da kayayyakin da darajar su takai ta naira milyan 6

0 75

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tace, tayi nasarar ceto rayukan mutane 60 da kayayyakin da darajar su takai ta naira milyan 6 da dubu dari bakwai, a hadarurrukan gobarar da aka samu a jihar cikin watan octoba.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi, shine ya bayyana adadin a zantawar sa da Kamfanin Dillancin labarai na kasa a jiya, a jihar ta kano.

Malam Abdullahi ya sanar da cewa, hukumar ta karbi kiran gaggawa 27 na tashin gobarar da aka samu a jihar cikin watan Octoban.

Kazalika ya bayyana cewa an rasa rayukan mutane 10 da kuma dukiyoyi na kimanin naira milyan 30 da dubu dari bakwai cikin watan na Octoba.

Saminu Abdullahi, ya alakanta tashin gobarar da ake samu a jihar, da rashin kulawa wajan amfani da tukunyar gas ta girki, da kuma rashin kulawa kan abubuwan amfani masu amfani da wutar lantarki.

Daga karshe ya shawarci iyaye da su dibga kulawa da motsin yaransu, da kuma hanasu zuwa kogi da sunan wanka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: