Hukumar Kiyaye Hadurra ta kaddamar da aikin sa-ido na musamman domin Sallar Layya a jihar Kano

0 223

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta kaddamar da aikin sa-ido na musamman domin Sallar Layya daga ranar Alhamis 5 ga Yuni zuwa Laraba 11 ga Yuni, 2025, da nufin rage haɗurran hanya da cunkoso a lokacin bukukuwan sallah.

Kakakin hukumar, Abdullahi Labaran, ya ce an shirya hakan ne duba da yawaitar zirga-zirgar ababen hawa a irin wannan lokaci.

A cewarsa, an tura jami’ai 1,889 da suka haɗa da Marshals na dindindin da na musamman tare da aiyukan agajin gaggawa a wurare daban-daban a fadin jihar, kana kuma an tanadi kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta masu karya dokokin hanya. Kwamandan hukumar, CC MB Bature, ya ja kunnen direbobi game da tuƙi cikin hatsari, ɗaukar kaya fiye da ƙima, da barazanar guje-guje a tituna, yana mai kira ga jama’a da su kiyaye dokokin hanya domin yin Sallah cikin aminci.

Leave a Reply