Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Jihar Jigawa Ta Yi Wa Sabbin Ma’aikata 15 Karin Girma

0 81

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Jihar Jigawa ta yi wa sabbin ma’aikata 15 karin girma da sabbin mukamai daban-daban.

Da yake makala kambu ga sabbin ma’aikatan da aka yi wa karin girma, kwanturolan hukumar na jiha, Ahmed Dauda Bagari ya taya su murnar samun karin girma.

Ya umarce su da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu.

Ahmed Dauda ya ce ba za a amince da zuwa a makare ba a hukumar, ya kuma shawarce su da su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa, inda ya ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin doka.

Kwanturolan ya ce sabuwar mukaddashiyar kwanturola janar ta hukumar ta zayyana wasu muhimman abubuwa guda uku da suka hada da gudanar da mulki, da fasfo da walwalar ma’aikata. Alhaji Ahmed Dauda ya ba da umarnin sake duba faretin ma’aikata na mako-mako da na wata-wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: