Hukumar kula da tsafta da ingancin abinci da kayan sha ta kasa (NAFDAC) ta kama wasu mutane 3 tare da katon 250 na gurbataccen Lemo a jihar Kano
Hukumar kula da tsafta da ingancin abinci da kayan sha ta kasa NAFDAC ta kama wasu mutane 3 tare da katon 250 na gurbataccen Lemo a jihar Kano.
An fara gano kayan ne a hannun wani mai suna Garba Yahaya dake Unguwar Kwana Hudu-Brigade a cikin birnin.
Hukumar ta kuma zarge shi da laifin sarrafawa tare da sayarwa al’umnma.
Babban ko’odinaton hukumar na jihar Kano Shaba Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin dayake zantawa da manema labarai a birnin kano, inda yace sun samu wannan nasarar bayan kama wasu matasa 3 dake tallan lemon, kuma bayan sun zurfafafa bincike ne suka kama wanda yake sarrafa lemon.
Idan zamu iya tinawa dai a watan Ramdana na shekarar data gabata, akalla mutane 10 ne suka mutu, aka kuma kwantar da daru-ruwa a asibibiti, bayan nuna alamun ciwon koda, biyo bayan shan wani Lemo marar inganci a jihar.