Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kwastam reshen jihar Kebbi, ta damke wata tirela dankare da fatar jaki da kudinta ya kai sama da naira miliyan 42.

Jami’in hukumar ya bayyana cewa motar na kan hanyar zuwa wata jiha a yankin Kudu maso Gabas.

Da yake zantawa da manema labarai jiya a hedikwatar hukumar da ke Birnin Kebbi, Kwanturolan Hukumar a Jihar, Joseph Attah, ya bayyana hakan a matsayin abinda ya sabawa doka.

Jospeh Attah ya bayyana cewa, an kama direban motar da wani a cikin motar wadanda ake zargi bisa lamarin.

Kwanturolan ya bayyana cewa hukumar ta Kwastam tana da cikakkiyar masaniyar cewa wasu ‘yan kasashen waje na zuwa kasarnan domin sayen fatar jaki domin amfanin a kasashensu da kamfanoninsu.

Joseph Attah ya yi alkawarin tabbatar da cewa sai an kama wadanda ke yin irin wannan haramtacciyar sana’ar, ta yadda zai kasance basu samu riba ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: