Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Kano zata kaddamar da gasar rubuce-rubuce kan annobar corona

0 84

Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Kano zata kaddamar da gasar rubuce-rubuce kan annobar corona a tsakanin daliban manyan makarantun jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina.

Daraktan lura da cutuka na hukumar, Dr Imam Wada Bello ya sanar da hakan ga manema labarai.

Yace an shirya gasar ne a tsakanin dalibai da nufin inganta hanyoyin karbar rigakafin cutar corona a tsakanin matasan arewa maso yamma.

Wada Bello wanda kuma shine shugaban kwamitin alkalin gasar yace gasar da asusun UNICEF mai kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina ya dauki nauyi yana da burin ganin an samu kashi 70 cikin 100 na alumma sun karbi rigakafin cutar.

Ya kuma bayyana muhimmancin da matasa suke dashi wajen cigaban harkokin kiwon lafiya a matakin farko.

Wada Bello ya kuma bukaci masu sha’awar shiga gasar su shiga shafin sadarwa na zamani domin duba kaidojin gasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: