Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da yarjejeniyar yaƙi da annobar korona tsakanin ƙasashe

0 438

Hukumar lafiya ta duniyar a ranar Litinin ta buƙaci ƙasashen duniya da su rungumi sabuwar yarjejeniyar da ta shafi yaƙi da annobar korona domin kaucewa maimaita abin da aka fuskanta a baya game da cutar.

Membobin hukumar ta WHO na gudana da taron shekara-shekara a helkwatar hukumar da ke birnin Geneva na ƙasar Switzerland.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, ” a wannan taro a bana muna fatan membobin hukumar lafiya ta duniya za su rungumi wannan sabuwar yarjejeniya”.

Ƙasar Amurka dai ta janye a matsayin memba daga hukumar na tsawon shekara ɗaya, matakin da ta ɗauka tun bayan da shugaban ƙasar Donald Trump ya kama aiki.

Wannan yarjejeniya da hukumar lafiya ta duniya ta fito da ita na neman tsarin haɗin kai ne tsakanin ƙasashen duniya wanda hakan zai taimaka wajen shirya wa tunkarar kowace annoba mai zuwa tare da gano muhimman ɓangarorin da ya dace a mayar wa hankali musamman wajen samar wa da isar da magungunna da alluran riga-kafi a wuraren da aka samu sake ɓullar annobar .

Kuma a ciki an fito da manufofin samar da daidaito tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da masu tasowa a wurin rabon rigakafin domin kauce wa abin da ya faru a lokacin ɓarkewar annobar COVID-19 a shekarun baya.

Leave a Reply