Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na fuskantar gibin kuɗin albashi da ya kai dala miliyan 500 a kasafin kuɗin shekara biyu masu zuwa, kamar yadda Darakta Janar ɗinta Tedros Ghebreyesus ya bayyana a taron babban zauren Majalisar Lafiya ta Duniya karo na 78 a Geneva.
Ghebreyesus ya ce sun ɗauki matakan rage kashe kuɗi ta hanyar hana yawan tafiye-tafiye, da sarrafa kayan aiki, da kuma rage ɗaukar ma’aikata da tura wasu ritaya kafin lokacinsu, don kare lafiyar kuɗin hukumar.
Hukumar ta ce matakan da ta ɗauka sun rage gibin, amma babu wata dabara da za ta hana rage yawan ma’aikatan. A yanzu dai, WHO na buƙatar ƙarin kuɗi domin ci gaba da aiki, kuma tana ƙoƙarin tsara sabon tsarin shugabanci wanda zai rage adadin sassanta daga 76 zuwa 34 tare da rage shugabanni daga 14 zuwa 7, don samun inganci da cin gashin kai.