Hukumar Lura da Safarar Ababen Hawa ta Jihar Bauchi (BAROTA) ta fara shirye-shirye daukar Matasa 250 aiki, wanda suka kunshi Kurata da Masu Mukamai domin inganta zirga-zirgar a hanyoyin Jihar.

Kakakin Hukumar Malam Dahiru Adamu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Bauchi.

A cewarsa, hukumar ta kaddamar da Shafin daukar Matasan da suke sha’awar shiga aiki, inda ya ce kawo yanzu kimanin Daruruwan takardun Matasan da ke son shiga aikin suka karba.

Malam Dahiru Adamu, ya ce daga cikin wadanda da zasu dauka din sun hada da Masu Sikandire 200 da Masu Digiri da HND 30 da kuma masu Takardun NCE da Diploma 20 a sassan Jihar.

Haka kuma ya ce Matasan da za’a dauka za’a tantance su a fannin Lafiya da kuma Halayya domin tabbatar da cewa sun cancanci aikin.

Kazalika, ya ce sabbin Ma’aikatan da za’a dauka zasu rika yin aiki hanyoyin Maraya da kuma na Karkara domin tabbatar da cewa babu wanda ya karya dokokin hanya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: