Hukumar masu yi wa ƙasa hidima ta hana matasa ɗalibai shiga sansanoninta har sai sun yi rigakafin cutar korona

0 99

Hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta hana matasa ɗalibai shiga sansanoninta har sai sun yi rigakafin cutar korona.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce shugaban NYSC Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce matakin zai fara aiki ne daga lokacin shiga sansanin horarwa mai zuwa nan da ‘yan makonni a ƙasa baki ɗaya.

Da yake yi wa jami’an hukumar da suka kula da Rukunin C na Tawagar II 2021 jawabi, Janar Ibrahim ya ce daga yanzu sai masu yi wa ƙasa hidima wato corp members sun nuna katin shaidar rigakafin kafin su shiga sansani.

Janar ɗin ya kuma gargaɗe su da daina yin balaguro cikin dare saboda tsaro, sannan ya ba su shawara da su dage da aikata abubuwan da suka koya a sansani don dogara da kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: