Hukumar NCDC ta ce mutum 80 ne suka sake mutuwa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa

0 64

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa NCDC ta ce mutum 80 ne suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar Zazzabin Lassa, ya zuwa jiya Alhamis.

NCDC ta bayyana wa taronta na bayar da rahoto kan barkewar cutar a Abuja cewa kawo yanzu an samu mutum 434 da suka kamu da cutar a fadin Najeriya.

A cewar sanarwar NCDC Daga watan Janairun 2021 zuwa yanzu, mutum 434 sun kamu da cutar, sannan mutum 80 sun mutu daga jihohi 17 da kananan hukumomi 63 da ke kasare nan.

Hukumar ta bayyana cewa Jihar Edo na da mutum 192, Ondo 150, Taraba 21, Ebonyi 17, Bauchi 15, sai Benuwai da jihar pilato mutum takwas kowanne.

Yayin da Kaduna ke dauke da mutum bakwai da suka kamu.

Sauran jihohin sun hadar da jihar Enugu da mutum 5, Nasarawa da Kogi na da mutane 3 kowanne, sai johohin Kuros Riba, Imo, Anambra da delita da Abia ke da mutum guda kowanne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: