Hukumar NCDC tace kimanin mutum 21 suka sake kamuwa da cutar Korona

0 54

Cibiyar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da cewa kimanin mutane 21 ne suka kamu da cutar corona a jiya litinin.

NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Internet, inda ansamu wadanda suka kamu da wannan cutar ne a Jihohin kasar nan 6.

Jihohin sunhada Lagos (6), Cross River (5), Rivers (5), Abia (3), Bauchi (1), and Kaduna (1).

A cewar ta a jiyan babu ko mutum 1 daya da cutar ta hallaka, amma akwai kimanin mutane dubu 2,976 da wannan cutar ta hallaka a fadin kasar nan tin bayan bullarta.

Ta kuma kara da cewa an sallami kimanin 38 daga wuraren killace masu wannan cutar a jiya litinin, bayan sun warke daga wannan cutar.

Kawo yanzu dai a kasar nan an tabbatar da cewa kimanin mutane dubu dari 214 da dari 113 ne suka kamu da wannan cutar, an kuma sallami mutane dubu dari 207 da dari 292 bayan sun warke daga cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: