Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce an samu rahotan bullar zazzabin Lassa guda 48 cikin wannan shekarar ta 2022.

Rahotan da Cibiyar ta fitar ya yi nuni da cewa an samu rahotan bullar cutar ne daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janeru da muke ciki.

Hukumar ta NCDC ta ce an samu rahotan ne a Kananan Hukumomi 22 na Jihohi 10 da suke kasar nan, ciki harda Bauchi da Edo da kuma Ondo.

Sauran Jihohin sune Taraba, Benue, Kaduna da Plateau da Kogi da Cross River da kuma Ebonyi.

Kwanaki kalilan da suka gabata, hukumar NCDC ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar samun barkewar cutar a kasar nan.

An bada rahotan cewa a shekarar 2021, kimanin mutane 102 ne suka mutu a sanadiyar zazzabin Lassar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: