Hukumar NDLEA ta gano kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 200 da ake zargi na almundahana a asusun DCP Abba Kyari

0 81

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta gano kimanin naira biliyan 4 da miliyan 200 da ake zargi na almundahana ne a asusun mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari da wanda ake tuhuma tare da shi, Sunday Ubua.

Sakamakon binciken hukumar ta NDLEA na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka mika wa ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’ah Abubakar Malami.

A cewar rahoton, hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta gano kudi naira biliyan 1 da miliya 400 ya shiga asusun Abba Kyari a lokacin da yake rike da mukamin kwamandan tawaga ta musamman mai kama barayi.

Sai dai asusun mataimakin Abba Kyari, Sunday Ubua, an gano kasa da naira biliyan 2 da miliyan 800.

Bincike ya nuna cewa Sunday Ubua ya karbi makudan kudade har naira biliyan 2 da miliyan 664 a ranar 15 ga watan Agusta, 2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: