Hukumar NDLEA ta gargaɗi mahajjata kan safarar miyagun ƙwayoyi zuwa kasa mai tsarki yayin aikin Hajji

0 94

Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa wato NDLEA ta gargaɗi mahajjata kan safarar miyagun ƙwayoyi zuwa kasa mai tsarki, a dai-dai lokacin mahajjatan ke haramar zuwa sauke farali.

Wata jami’ar a hukumar Habiba Zubair tayi wannan gargaɗi a birnin Illori na Jihar Kwara a lokacin da take jawabi ga mahajjatan bana.

Ta yi gargaɗin cewa magungunan da likitoci suka bayar da izinin sha kaɗai za a iya tafiya da su, inda ta ce duk wani abu koma bayan hakan gwamnatin Saudiyya ba za ta lamunta ba.

Ta cigaba da gargadin mahajjatan kan safarar goro ko kuma barkwano zuwa kasa mai tsarki, ta kuma yi kira ga mahajattan da kada su kuskura wani ya karɓi kayan wani ajiya ko riƙo sakamakon za a iya ɓoye wasu abubuwan da aka haramta a cikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: