Hukumar NDLEA ta kama mutane 679 bisa zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar Jigawa

0 74

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a Jihar Jigawa ta kama mutane 679 bisa zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi, tare da kwace kwayoyi masu nauyin kilogiram 325.06 daga watan Yunin bara zuwa yanzu.

Kwamandan Hukumar na Jihar Jigawa, Ibrahim Braji ya bayyana haka a taron manema labarai, gabanin bikin ranar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta duniya wadda majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni na kowace shekara.

Ibrahim Braji yace daga adadin mutane da aka kama bisa zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi, 617 maza ne yayin da 8 suka kasance mata.

Kwamandan ya ce da goyon bayan gwamnatin jihar Jigawa da sauran hukumomin tsaro, hukumar ta fadada ayyukanta zuwa dukkanin kananan hukumomi 27 na jiharnan.

Ibrahim Braji ya yabawa gwamnan jiha, Muhammadu Badaru Abubakar, da shugabannin kananana hukumomi da sauran hukumomin tsaro bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen samun nasarar hukumar a yakin da take wajen kakkabe dabi’ar ta’ammali da miyagun kwayoyi da safararsu a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: