Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jiya ta lalata kwayoyi da nauyin su ya kai kilogram 20,00 masu darajar naira miliyan 50 a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar na kasa Brig.-Gen. Buba Marwa ne ya bayyana hakan a lokacin kona kayan mayen a bainar jama’a a Abuja, inda ya jaddada kudirin hukumar na yaki da wannan dabiar a fadin kasar nan.

Marwa, wanda sakataren hukumar Bar. Shadrach Haruna ya wakilta, yace girman adadin yawan wannan kwayoyin ya tabbatar da cewa akwai kalubale sosai wajan yaki da sha da fatucin miyagun kwayoyi.

Kafin hakan dai kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa shugaban kasa ya kaddamar sabon tsari da yayi masa take da yaki akan miyagun kwayoyi a ranar 26 ga watan Yuni domin yaki da dabi’ar a fadin kasar nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: