Hukumar NDLEA ta nemi hadin kan ‘yan Najeriya a yakin da take yi da matsalar shan muggan kwayoyi

0 66

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta nemi hadin kan ‘yan Najeriya a yakin da take yi da matsalar shan muggan kwayoyi.

Shugaban hukumar Mohammed Buba-Marwa ne shine ya yi wannan kiran yau a Abuja a wajen bikin cika shekaru 20 da kafa wata cibiyar matasan Najeriya.

Kazalika bikin ya zo daidai da kaddamar da yakin da ake yi da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma rashin tsaro a fadin kasarnan, daga shugaban na cibiyar, Ibrahim Haruna.

Buba-Marwa, wanda Darakta mai gabatar da kara da ayyukan shari’a na hukumar, Joseph Sunday ya wakilta, ya ce hukumar ita kadai ba za ta iya yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi ba tare da hadin kan jama’a ba.

Buba Marwa ya bayyana cewa kashi 14.4 bisa 100 na ‘yan Najeriya ne ke shan muggan kwayoyi kuma hakan ya ninka matsakaicin adadin da ake samu a duniya har kusan sau 3.

Leave a Reply

%d bloggers like this: