

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Hukumar jarabawar kasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar external ta bara, inda aka rike sakamakon dalibai dubu 4 da 454 saboda laifukan satar amsa daban-daban.
Sakamakon, wanda aka saki kwanaki 64 bayan an rubuta jarabawar karshe, kashi 78 cikin 100 sun samu nasara.
Magatakardar hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Wushishi, wanda ya sanar da haka a helkwatar NECO dake Minna a jihar Neja, yace an soke aikin masu sanya ido a jarabawa su 4.
Dantani Wushishi yace dalibai dubu 49 da 916 ne suka yi rijistar jarabawar ta watan Nuwamba zuwa Disamba, inda ya kara da cewa dalibai dubu 36 da 116 daga cikin dubu 45 da 821, wato kashi 78.04 cikin 100, sun samu credit zuwa a harshen Turanci.
Yace dalibai dubu 35 da 706 daga cikin dubu 45 da 756, wato kashi 78.04 cikin 100, sun samu credit 5 zuwa sama ciki har da lissafi.