Hukumar Nema ta ce za ta tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin kasa

0 284

Hukumar kai ɗaukin gaggawa ta kasa (Nema) ta ce za ta tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin kasa domin kare su daga ‘ɓata-gari’

Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan wani daga cikin rumbunanta da ke Abuja, a jiya Lahadi.

Wasu matasa ne ake zargin sun kai farmaki kan rumbun wanda ke unguwar Gwagwalada da ke birnin, inda suka yi awon-gaba da kayan abinci da kuma sauran abubuwan da aka taskace a rumbun.

Kamar yadda wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Manzo Ezekiel, ta bayyana cewa.

Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziƙi, inda mutane da dama ke kokawa kan rashin abinci da tsadar kayan masarufi.

Kafin fasa rumbun ajiye abincin a Abuja, an samu rahotannin yadda mutane suka far wa motocin dakon kayan abinci tare da wawase abin da suke ɗauke da shi a wasu yankuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: