Hukumar NEMA ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu a fashewar da ta auku a wata haramtacciyar matatar mai a jihar Imo sun karu zuwa 110

0 29

Hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu a fashewar da ta auku a wata haramtacciyar matatar mai a jihar Imo sun karu zuwa 110.

Mukaddashin shugaban ayyukan hukumar na jihoshin Imo da Abia, Ifeanyi Nnaji, shine ya sanar da haka a jiya ga kamfanin dillancin labarai na kasa.

Ifeanyi Nnaji yace sun sake gano karin gawarwaki a kogin Orashi kusa da inda lamarin ya auku ranar Lahadi, yayin da wasu suka mutu a asibitoci daban-daban, lamarin da ya kara yawan adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu.

Wata haramtacciyar matatar mai a dajin Abaeze na jihar Imo ta kama da wuta a ranar Juma’a da dare inda ta jawo mutuwar mutane 100.

Ma’aikatan ceto a jihar Imo, karkashin shugabancin Ifeanyi Nnaji sun isa wajen tun bayan aukuwar lamarin domin aikin ceto tare da kwaso gawarwaki.

Babban jami’in na NEMA ya kara da sanarwa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa ana shirye-shiryen binne gawarwakin a lokaci daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: