Hukumar NITDA ta bukaci a bawa Mutanen da ke da Bukata ta Musamman dama a tsare-tsaren Fasahar Sadarwa
Hukumar NITDA Ta Bukaci A Bai Wa Mutanen Da Ke Da Bukata Ta Musamman Dama a Tsare-Tsaren Fasahar Sadarwa
Shugaban Hukumar Raya Fasahar Sadarwa ta Ƙasa, Malam Kashifu Abdullahi, ya bukaci da a tabbatar da shigar da mutane fiye da miliyan 35 da ke da bukatu na musamman cikin dukkan tsare-tsaren ci gaban fasaha a kasar nan.
A yayin wata ziyara da kungiyar masu bukata ta musamman, Inclusive Friends, ta kai, Kashifu ya bayyana cewa ba za a cimma nasarar da ake bukata ba idan aka bar wannan rukuni a baya.
Ya ce a halin yanzu fiye da kashi 60 cikin 100 na mata masu nakasa ba su san yadda ake kunna kwamfuta ba, balle amfani da kayan aikin fasaha, lamarin da ke kara hana su damar samun aiki da hadewa da sauran jama’a.
Kungiyar Inclusive Friends ta sha alwashin mikawa hukumar NITDA shawarwarin da suka fito daga tarurrukan tattaunawa da nufin ganin an gyara matsalolin da ke hana wannan rukuni shiga cikin tafiyar dijital ta Najeriya.