Hukumar NJC ta soke nadin justice Theophilus Nzeukwu a matsayin babban alkalin jihar imo

394

Hukumar shari’a ta kasa, NJC, ta soke nadin Justice Theophilus Nzeukwu a matsayin mukaddashin babban alkalin jihar Imo, tana mai umartar Gwamna Hope Uzodinma da ya nada babban jami’i mafi daraja a matakin kotun koli bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Hakanan NJC ta umarci Justice Nzeukwu da ya bayyana dalilin da yasa bai kamata a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba, tare da ladabtar da Justice V.U. Okorie bisa jagorantar taron da ya bada shawarar nadin ba bisa ka’ida ba.

A wani mataki na tsaftace bangaren shari’a, NJC ta dakatar da wasu alkalai uku, ciki har da Justice Jane Inyang na kotun daukaka kara, bisa zargin amfani da mukami ta hanyar bayar da umarnin da ban a daidai ba.

NJC ta kuma bayyana matakin bude shafin bayyanar sunayen wadanda ake tantancewa domin nada su a matsayin alkalai, don bai wa jama’a damar tofa albarkacin bakinsu kan sahihancin da amincin wadanda za a nada.

Comments are closed.

hitta mer om recensioner