Hukumar Sadarwa ta Kasa NCC ta ce za ta kaddamar da fasahar shiga intanet ta 5G zuwa watan Agustan bana

0 81

Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, ta ce za ta kaddamar da fasahar shiga intanet ta 5G zuwa watan Agustan bana.

Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Dambatta ne ya bayyana haka a taron majalisar masu amfani da wayar tarho karo na 90 da aka gudanar jiya a Legas.

Umar Dambatta ya ce hukumar NCC, ta hanyar tallafin ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta tarayya, za ta tabbatar da fara amfani da fasahar don kara habaka ci gaban ayyukan sadarwa a kasarnan.

Ya ce bisa la’akari yawan mutanen kasarnan kimanin miliyan 214; tare da karuwar jama’a da ake samu da kashi 2.6 a kowace shekara a takaice, kimanin kashi 76.46 na yawan al’umar kasarnan zasu kasance cikin rukunin ‘yan kasa da shekaru 35.

Umar Dambatta ya nanata cewa, burin hukumar shi ne Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen amfani da fasahar 5G wadda domin amfanin masu ruwa da tsaki da kuma bayar da gudunmawa sosai ga manufofin gwamnatin tarayya kan tattalin arziki na zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: