Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa zata dauki mutane 50-50 daga duk jihohin Najeriya

0 134

Hukumar Samar da ayyukan yi ta kasa a jiya ta ce kimanin mutane 50-50 daga jihohin kasarnan 25 da kuma babban birnin tarayya ne za su ci gajiyar shirin shirin samar da ayyukan yi na noma na hukumar a kashi na biyu.

Hukumar ta ce hakan ya yi daidai da kokarin gwamnatin tarayya na samar da guraben ayyukan yi ga masu fama da matsalar rashin aikin yi a Najeriya, da kuma habaka tattalin arzikin kasarnan.

A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Edmund Onwuliri, a kashi na farko, jihohi 12 ne suka ci gajiyar irin wannan shirin a lokacin gwaji.

Jihohin da za su ci gajiyar shirin a halin yanzu sun hada da Jigawa, Kano, Yobe, Gombe, Kaduna, Kebbi, Zamfara, Borno, Bayelsa, Benue, Bauchi da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: