Hukumar tace fina-finai ta haramta nuna fina-finan da suke nuna yadda ake garkuwa da mutane

0 65

Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta nuna fina-finan da suke nuna yadda ake Garkuwa da mutane, shan miyagun kwayoyi da kuma kwacen waya a jihar.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Malam Ismaila Na’aba Afakallah, shine ya bayyana hakan, inda ya ce haramtawar ta zama dole biyo bayan yadda aikata hakan ya zama ruwan dare a cikin Al’umma.

A cewarsa, daga yanzu hukumar bazata lamuncin nuna fina-finan da suka kunshi Garkuwa da mutane, ko kwacen waya ba, ko kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar ta Kano.

Afakallah, ya ce sun dauki matakan ne domin dakile matsalolin da suke cigaba da yaduwa a tsakanin Matasa wanda suke cigaba da aikata laifuka.

Shugaban hukumar ya ce matukar matasa suna ganin yadda abubuwan suke wakana, zasu cigaba da aikata laifukan.

Kazalika, ya ce daukar matakan sun zama dole kafin lokaci ya kurewa hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: