Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta soke lasisin aiki na wasu gidajen disko da nishaɗi guda takwas da ke jihar
Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta soke lasisin aiki na wasu gidajen disko da nishaɗi guda takwas da ke faɗin jihar, tare da haramta musu cigaba da aiki har abada.
Sakataren zartarwa na hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba. Ya ce wannan mataki wani bangare ne na kokarin hukumar wajen tsarkake masana’antar nishaɗi da kare dabi’un al’umma bisa tsarin addini da al’adun Kano.
A cewarsa, cibiyoyin da aka haramta sun aikata ayyuka da ke lalata tarbiyya, kamar shirya tarukan dare mara tsari, nuna abubuwan batsa, da kuma gudanar da ayyuka ba tare da izinin hukumomi ba.
Gidajen nishaɗin da aka soke lasisinsu sun haɗa da, Hamdala Entertainment, Lady J Entertainment, Dan Hausa Entertainment, Ni’ima Entertainment, Ariya Entertainment, Babbangida Entertainment, Harsashi Entertainment da kuma Wazobiya Entertainment
El-Mustapha ya gargadi masu kamfanonin da su guji yunkurin sake buɗe ayyukansu da wani suna ko ta wata hanya, yana mai cewa hakan zai jawo musu fuskantar matakan doka da hukunci.
Hukumar ta ce zata cigaba da gudanar da bincike da sa ido a dukkan sassan jihar domin tabbatar da cewa masana’antar nishaɗi tana tafiya daidai da tsarin da aka gindaya.