Hukumar tsaron fararen hula na Civil Defense ta tarwatsa wasu gungun barayin babura dake addabar mutanen karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa

0 65

Hukumar tsaron fararen hula civil defense ta tarwatsa wasu gungun barayin babura dake addabar mutanen karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin jiha.

Yace jami’an hukumar sun samu nasarar kama mutane biyu daga cikin ‘yan gungun, bisa hannu a sata da hada baki wajen cin amana, lamarin da ya sabawa sashe na 97 da 286 na kundin manyan laifuffuka.

Adamu Shehu yace wadanda aka kama sun hada da Mamman Garba mai shekaru 24 da abokiyar aika-aikarsa mai suna Ummi Sa’adu, ‘yar shekara 20.

Yayi bayanin cewa an kama wadanda ake zargi biyo bayan wani korafi da aka kai ofishin hukumar na Jahun, cewa wadanda ake zargin sun kware waje yaudarar wadanda suke yiwa sata.

Wadanda ake zargin sun amince cewa sun gudu da babura 6 kala-kala tare da sayar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: