Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta kasa ta ce cutar kwalara ta kashe mutum 233 a Najeriya

0 69

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta kasa (NCDC) ta ce cutar kwalara ta kashe mutum 233 a jihohi 31 na ƙasar.

Sannan hukumar ta ce an samu jimillar mutum dubu 10,217 waɗanda suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

Shugaban hukumar Dr Ifedayo Adetifa ne ya bayyana hakan sa’ilin da ya yi bayani kan halin da ake ciki a ɓangaren lafiya na ƙasar nan.

Ya ce a watan Agusta an samu ƙaruwar kimanin kashi 47% na yawan masu kamuwa da cutar idan aka kwatanta da watan Yuli da ya gabata.

A cewarsa ya zuwa yanzu an tabbatar da cewa mutane 933 sun kamu da zazzaɓin Lassa, yayin da zazzaɓin ya yi sanadiyyar rayukan mutane 173.

Haka kuma mutane dubu 1,180 ne ake zargin sun kamu da cutar kyandar biri, yayin da cutar tayi sanadiyyar rayuka 481 cikin wannan shekara.

Wannan dai na zuwa ne a gabar aka bayyana Najeriya a matsayin kasa ta daya a cikin jerin kasashen da duka fi fama da tarin fuka a nahiya Africa kuma itace 6 a duniya baki daya, a cewar babban daraktan gidauniyar KNVC Dr Berthrand Odume, wanda ya bayyana haka a wani sansanin yan gudun hijra na 3 dake Daudu a karamar hukumar Guma ta jihar Benuwai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: