Shugaban hukumar ‘yan sanda, Solomon Arase, ya kafa kungiyar tuntubar jami’an ‘yansnada da suka yi ritaya.
Solomon Arase, wanda tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda ne ya bayyana haka a wajen taron farko na kungiyar jiya a Abuja.
Ana sa ran kungiyar za ta kasance cibiyar nazari ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda domin inganta harkokin tsaro a sassan kasarnan.
Solomon Arase ya bayyana cewa ya kamata a mutunta ilimin aiki da ‘yancin kai na Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ba tare da amincewa ko tauye ikon sa ido na hukumar kan ‘yan sanda ba. Ya bayyana kudurinsa na ganin rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda suna aiki tare da juna domin ci gaban rundunar baki daya, tare da mai da hankali kan kawo sauyi a harkokin tsaro ta hanyar horaswa da sake horas da jami’an ‘yansanda.