Hukumar zaɓe ta ƙasar Libya ta yi kira da ɗage zaɓen shugaban ƙasa da ya kamata a gudanar a ranar Juma’a

0 347

Hukumar zaɓen ta Kasar Libya ta yi kira da ɗage zaɓen shugaban ƙasa da ya kamata a gudanar a ranar Juma’a mai zuwa.

Hukumar na son a ɗage zaɓen na tsawon wata ɗaya, kuma ta ba da shawarar gudanar da zaɓen a ranar 24 ga watan Janairu bayan tuntuɓar majalisa.

Zaɓen Libya na tattare da ƙalubale musamman cancantar wasu ƴan takarta da kuma barazanar tsaro.

Tun mutuwar Kanal Ghaddafi a 2011 Libya ke fama da rikici. Daga cikin waɗanda aka hana takara har da ɗan tsohon shugaban Saif al-Islam.

Jakadan Kasar Amurka a Libya Rochard Norland, ya bayyana damuwa a madadin Amurka bisa dage lokacin zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: