Hukumar zabe ta INEC zata kar naurori da ma’aikata na musamman biyon bayan bukatar da majalisar wakilai tayi na kara wa’adin mallakar katin zabe

0 82

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata kar naurori da ma’aikata na musamman, biyon bayan bukatar da majalisar wakilai tayi na kara wa’adin mallakar katin zabe na din-din.

Shugaban kwamitin Zabe a zauran majalisar Aisa duku, Itace ta bayyana haka a lokacin da take yiwa zauran majalisar sakamakon tattaunawar da sukayi da hukumar zaben mai zaman kanta.

A ranar 15 ga watan June ne majalisar wakilan ta umarci kwamitin da ya gana da hukumar zaben biyo bayan kudirin da wani dan majalisa ya bayar.

Majalisar ta bukaci hukumar zaben da ta tsawaita wa’adin yin rijistar katin zaben zuwa kwanaki 60.

Yan majalisar sun lura da cewa akwai adadi mai yawa na wadanda suka isa yin zabe amma basu mallaki katin zaben ba, duk da cewa akwai cibiyoyin yin rijistar masu yawa.

Da farko dai an tsara za’a rufe yin rijistar katin zaben a karshen watan nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: