Hukumomi a Najeriya sun kama mutum uku bisa zargin safarar namun daji da cinikinsu ba bisa ƙa’ida ba

0 297

Hukumar da ke sa ido kan ayyukan da suka shafi kare muhalli ta (NESREA) tare da hukumar kula da gidajen ajiyar dabbobin daji ta ƙasa ne suka yi kamen ranar Talata a Abuja a wani samamen haɗin gwiwa.

Wata sanarwa daga jami’ar hulda da jama’a ta NESREA, Nwamaka Ejiofor, ta ce an kama waɗanda ake zargi a sassa daban-daban na birnin saboda sayar da tsuntsaye da dabbobin daji da aka haramta, wanda ya saɓa dokar kare dabbobin da ke fuskantar barazaar ƙarewa.

Shugaban NESREA, Farfesa Innocent Barikor, ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa safarar dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙarewa laifi ne a karkashin dokar ƙasar, yana mai gargaɗin cewa za a gurfanar da duk wanda aka kama da irin wannan laifi a gaban kotu.

Leave a Reply