Hukumomin Saudiyya sun nanata cewa sun ɗauki matakai domin rage wa mahajjata wahalhalu na zafin rana a Hajjin bana yayin da ake tsammanin zafin zai ci gaba da ƙaruwa.
A shekarar da gabata, mutane 1,300 ne suka mutu yayin aikin akasari saboda zafin mai tsanani a birnin Makkah.
An shuka dubban binshiyoyi da kuma kakkafa ɗaruruwan na’urorin sanyaya wuri domin rage ɗumin da aka yi hasashen zai kai 44C a ma’auni.
Sun kuma hana yara ‘yan ƙasa da shekara 12 yin aikin ibadar. Kazalika, sun jibga tara da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama yana yunƙurin shiga Makkah ba tare da cikakken izini ba. Zuwa ranar Lahadi, hukumomi sun ce sun hana mutane fiye da dubu 269,000 shiga birnin na Makkah, wanda shi ne mafi tsarki a addinin Musulunci.