Hukuncin da za a yankewa wanda ya kashe Hanifa mai tsauri ne – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano

0 140

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wani malamin makaranta mai zaman kanta, mai suna Abdulmalik Tanko, wanda ake zargi da yin garkuwa tare da kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekaru biyar.

Ana zargin Abdulmalik Tanko da hada baki da wani mai suna Hashim Isyaku, wanda shi ma yake tsare a hannun ‘yansanda.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar jiya, ya ce wadanda ake zargin sun bukaci iyayen yarinyar da su biya kudin fansa naira miliyan 6.

Hanifa dalibar Abdulmalik Tanko ce a wata makaranta mai zaman kanta da ke Kwanar Dakata a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

A cewar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya amsa laifin sa na bawa yarinyar guba a lokacin da ya fahimci cewa ta gane shi.

Daga nan Abdullahi Tanko da Hashim Isyaku suka binne gawarta a wani karamin kabari da suka haka a harabar makarantar da ke Kwanar ’Yan Gana, a Unguwar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: