Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya fi dacewa ya jagoranci kasarnan a shekarar 2023.

Babangida ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Osibanjo Grassroot a gidansa da ke Hill Top a Minna, babban birnin jihar Neja.

Ya bukaci Farfesa Osinbajo ya ci gaba da mayar da hankali da nuna juriya.

Tsohon shugaban na soji ya shaida wa kungiyar cewa ya amince ya yi magana da ‘yan kungiyar ne saboda mutuncin mataimakin shugaban kasa da kuma tabbatar da cewa Osinbajo na da abin da ya kamata ya jagoranci kasarnan.

Babban shugaban kungiyar na kasa, Ojo Foluso, ya ce kungiyar ta yi farin ciki da kalaman Babangida.

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da matsa wa mataimakin shugaban kasar lamba kan ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: