‘Ina da dalilan da yasa zanbar jam’iyyar PDP’ – Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

0 56

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar NNPP.

An sanar da yadda Kwankwaso ya tattauna da shugabannin NNPP kwanakin baya.

A wata hira da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce shirye-shirye sun yi nisa kuma zai bayyana matakin da zai dauka kafin karshen watan Maris.

Duk da dai bai bayar da cikakken bayanin dalilan komawa NNPP ba, a kwanakin baya Kwankwaso ya ce APC da PDP ba su da wani abin da za su baiwa ‘yan Najeriya a shekarar 2023.

Shima da yake zantawa da Sashen Hausa na BBC, wani na hannun damar tsohon gwamnan, ya ce rashin magance rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP a jihar Kano ne ya tilastawa Kwankwaso ficewa daga jam’iyyar.

A watan jiya ne Kwankwaso ya hada kai da wasu mukarrabansa domin kaddamar da wata tafiya ta kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: