Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da halin rikici da jam’iyyun adawa da dama na ƙasar ke ciki.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin jawabin da ya yi na ranar tunawa da dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis.
“Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a tagayyare,” kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.
Tinubu ya ce “ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin dadin ganin ku a haka.
Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ke ci gaba da karɓar ƴan siyasa masu sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.
Tinubu ya ce jam’iyyar APC ba za ta hana kowa shiga cikinta ba domin yin hakan tauye hakkin al’umma ne.