Mamallakin makaranta a Kano, Abdulmalik Tanko, da ake tuhuma a gaban kotu tare da wasu bisa zargin sacewa da kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar, a jiya ya fara kare kansa inda ya musanta aikata laifin.

Abdulmalik Tanko mai shekaru 34 tare da Hashimu Isyaku dan shekara 37 da Fatima Musa mai shekara 26, dukkaninsu mazauna unguwar Tudun Murtala a Kano, suna fuskantar shari’ah a gaban babbar kotun jihar Kano.

Ana tuhumarsu da aikata laifuka 5 na cin amana da garkuwa da mutane da kisa da boye gawar yarinyar mai shekaru 5.

Bisa jagorancin lauyansa, Abdulmalik Tanko yace shi da sauran mutane biyun da ake tuhuma, basu da masaniyar yadda Hanifa ta mutu.

Alkalin, mai shari’ah Usman Na’abba, ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Mayu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: