Labarai

Ina yabawa shugaba Buhari bisa yadda yake tafiyar da harkokin tsaro lafiya da sauran magance kalubalen da ke fuskantar Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na matukar godiya ga tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, bisa jajircewarsa na ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasarnan.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, ya ce shugaban kasar wanda ya zanta da Ban ta wayar tarho jiya ya sake jaddada girmamawa da kuma jin dadinsa ga ayyukan tsohon babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma godewa Ban Ki-Moon bisa kiransa a waya.

A nasa bangaren, Ban Ki-Moon ya yabawa shugaba Buhari bisa yadda yake tafiyar da harkokin tsaro da magance kalubalen da ke fuskantar kasar.

Ya nuna jin dadinsa da goyon bayan da wasu fitattun ‘yan Najeriya biyu suka ba shi; Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin sakatare-janar ta Majalisar Dinkin Duniya, da Amina Mohammed, mataimakiyar sakatare janar ta yanzu, inda ya ce suna daga cikin mutane mafiya nagarta da ya taba yin aiki da su a rayuwarsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: