Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ana samun jinkiri wajen gudanar da zabuka 17 na cike gurbi a faɗin ƙasar nan saboda ƙarancin kuɗi.
Wadannan zabukan sun shafi mazabu 17 da ke cikin kananan hukumomi fiye da 32, da yankunan rajistar zabe 359 da kuma fiye da rumfunan zaɓe 7,000.
Duk da cewa hukumar ta tanadi kusan Naira biliyan 126 a kasafin kudinta na shekarar 2025, ba ta samu amincewa daga sashen da ya shafi zabukan cike gurbi ba. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sha bayyana cewa babu tanadi na kudin zabukan cike gurbi a kasafin kudin bara, kuma hakan na janyo wa hukumar ƙalubale, musamman ganin yadda yawansu ke ƙaruwa sanadiyyar murabus da rasuwar ‘yan majalisa.