Jakadun ƙasashen Yamma guda biyar sun nema Najeriya ta gaggauta gyara dokar laifukan sadawar na Intanet

0 173

Jakadun ƙasashen Yamma guda biyar sun bukaci Gwamnatin Tarayyar da ta gaggauta gyara Dokar Laifukan Sadarwa ta Intanet da aka kafa a 2015, suna cewa ana amfani da dokar ne wajen murƙushe ’yancin faɗar albarkacin baki da hana cigaban tattalin arzikin ƙasa.

A wata sanarwa da suka fitar don tunawa da ranar Dimokiraɗiyya, wakilan Amurka, Birtaniya, Finland, Norway da kuma Kanada sun nuna damuwarsu game da yadda rashin fayyace dokar ke bawa hukumomi damar kama ’yan jarida da masu fafutuka irinsu Dele Farotimi.

Duk da cewa gwamnati ta sha alwashin nazarin dokar, jakadun sun ce sai an tsara tanade-tanadenta bisa tsarin doka da ƙa’idar dimokiraɗiyya kafin a samu sauyi mai ma’ana.

Sun kuma bukaci majalisa da ta fifita gyaran, ta bude hanyoyin tattaunawa tare da tabbatar da cewa an dace da ƙa’idodin duniya.

Leave a Reply