Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta ce ba za a tsawaita wa’adin aikin rajistar jarabawar ba, wacce aka tsara kammalawa a ranar 26 ga Maris.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya ta hannun shugabanta na hulda da jama’a, Dr Fabian Benjamin a Abuja.

Fabian Benjamin ya ce lokacin da aka tsara gudanar da aikin rajistar daga ranar 19 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga Maris, shi ne kawai wa’adin da hukumomin da abin ya shafa suka baiwa hukumar domin gudanar da aikin rijistar.

Ya kara da cewa, ba haka kawai aka kayyade ranakun rajista da jarrabawar ba, sai dai aka samu amincewar ra’ayoyin ma’aikatar ilimi ta tarayya da hukumomin jarabawar daban-daban.

Ya kara da cewa kafin a fara rajista ko jarrabawar ta kowace shekara, sai an gayyaci dukkanin hukumomin da za su gudanar da jarrabawar zuwa wani teburi, inda za su amince da jadawalin gudanar da ayyukan kowace hukumar jarrabawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: