Jamb ta gargadi dalibai da su dena karbar admission ta hanyar da bata dace ba

0 59

Hukumar samar da guraben karatu a manyan makarantu (JAMB) tace baza ta cigaba da lamuntar bayar da guraben karatu ta hanyar da bata kamata ba, daga manyan makarantu, inda ta gargadi dalibai da su kauracewa karbar gurbin karatu daga makarantu ba ta karkashin tsarin CAPS na hukumar JAMB ba.

Hukumar jarabawar ta bayar da gargadin a wani sakon shawarwari da ta aikawa shugabannin manyan makarantu, wanda kuma aka wallafa a jaridar hukumar ta mako-mako.

Hakan ya biyo bayan gargadin hukunci da a baya ministan ilimi, Adamu Adamu, yayi, dangane da abinda ya kira rashin bin umarni da wasu shugabannin manyan makarantu ke yi, wadanda ake zargin suna cigaba da take umarnin ministan dangane da batun.

Hukumar ta JAMB tace makarantun da har yanzu suke talla da sayar da takardun daukar dalibai, ana basu shawarar su kauracewa aikata hakan.

Sakon, daga nan, ya hori makarantun da abin ya shafa su karfafa gwiwar dalibansu da su nemi gurbin karatu ta karkashin hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: