Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ce dakarunta sun yi arangama da takwarorinsu na kasar Rwanda

0 81

Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ce dakarunta sun yi arangama da takwarorinsu na kasar Rwanda a kusa da iyakar kasa ta gabas a jiya.

Mai magana da yawun sojojin a lardin Kivu ta Arewa ya ce sojojin Rwanda sun tsallaka zuwa kasar Congo kuma tashin hankali ya kai ga rikici.

Sojojin Rwanda ba su mayar da martani kan wannan zargi ba.

Bidiyoyin da ke yawo a shafukan internet sun nuna mutanen yankin cikin firgici suna tserewa yayin da bangarorin dakarun biyu ke musayar wuta. Daga baya sojojin Rwanda sun koma gida.

Shugabannin yankin sun ce mazauna garin sun koma gidajensu bayan an samu kwanciyar hankali.

Rikicin kan iyaka tsakanin makwabtan kasashen biyu na Gabashin Afirka ya zama ruwan dare, saboda haramtacciyar cinikayya, da rashin tsayayyar iyakar kasashe, hade da hare-haren ‘yan tawaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: