Jami’an Gwamnatin jihar Jigawa za su ziyarci kasuwanni da kauyuka domin wayar da kan al’umma muhimmancin bayar da kudaden shiga

0 72

Jami’an Gwamnatin jihar Jigawa za su ziyarci kasuwanni da kauyuka domin wayar da kan al’umma muhimmancin bayar da kudaden shiga.

Wakili a kungiyar tabbatar da adalci kan karbar kudaden shiga Dr Sa’id Umar shine ya bayyana hakan ta cikin wani shirin radio Jigawa.

Sa’id Umar wanda ya gabatar da kasida a taron farko da gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar kan muhimmancin karbar kudaden shiga, ya bayyana muhimmancin da karbar kudaden shiga yake dashi ga kowacce gwamnati.

Yace ‘yan kasuwa da talakawa da ma’aikata suna biyan kudaden shiga domin kara bai wa gwamnati dama wajen gudanar da muhimman ayyukan raya kasa.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar tuntuba kan kudaden shiga na jiha, Muhammad Abdu Dutse, yace suna bibiyar kudaden shiga da gwamnati ta tara domin amfanin al’umma.

A jawabinsa, shugaban kungiyoyin kyautatuwar zaman jama’a na jihar Jigawa, Comrade Musbahu Basirka yace biyan kudaden shiga yana tabbatar da bin doka da oda inda yace kungiyoyi zasu cigaba da wayar da kan al’umma muhimmancin bayar da kudaden shiga domin inganta rayuwa da zamantakewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: