Jami’ar Tarayya da ke Gashua a Jihar Yobe, ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 927 a zangon karatu na 2024/2025.
Bikin na kaddamarwa ya kunshi sabbin ɗalibai daga sassa daban-daban na jami’ar, ciki har da tsangayar koyon aikin Noma, da Harsuna da Fasaha, Kimiyya, da Harkokin Tattalin Arziki na zamani.
A jawabin da ta gabatar a yayin taron da aka gudanar a harabar jami’ar a jiya, Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta taya sabbin ɗaliban murna bisa samun nasarar shiga jami’ar, tare da ƙarfafa mu su gwiwa wajen gudanar da karatunsu cikin da’a, hazaka da kuma gaskiya.
Farfesa Waziri ta sake jaddada kudirin jami’ar wajen samar da yanayi mai kyau da tallafi ga ɗalibai domin samun ilimi da kwarewa da za su taimaka musu su yi fice a fagen ilimi da kasuwanci a matakin duniya.
Sai dai ta gargaɗi ɗaliban da su nisanci halayen banza da dabi’un rashin kirki kamar yin maguɗi a jarrabawa da sauran laifuka, tana mai cewa jami’ar ba za ta lamunci irin waɗannan abubuwa ba.
Ta kuma shawarci ɗaliban da su amfana da Asusun Rancen Ilimi na Ƙasa (NELFUND), shirin Gwamnatin Tarayya da ke da nufin bunƙasa samun damar shiga manyan makarantu ga kowane ɗalibin Najeriya.
Ta bayyana cewa waɗanda suka cancanta za su iya tuntuɓar jami’in hulɗa da NELFUND a sashen kula da harkokin ɗalibai don samun cikakken bayani da jagoranci.