Jam’iyar APC a Jihar Jigawa ta kaddamar da Kwamatin Sasanto da Bada Hakuri ga Yayan Jam’iyar da aka Batawa a zaben fidda Gwani wanda aka gudanar domin dakile sauyin sheka, karkashin Jagorancin Senator Bello Maitama.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, ya amince da kaddamar da Kwamatin mai Mambobin 27 domin hakurkurtar da mutanen da suka yi Takara a Jam’iyar da kuma wadanda aka batawa a zabukan fidda Gwani na yan takarar Gwamna, da Majalisun Jihar da Matakin Kasa.

Kwamatin zai biyiyi yayan Jam’iyar APC da suka yi Takara amma basu samu nasara ba, kuma suke kokarin barin Jam’iyar.

Kungiyar Cigaban Demokradiya ta bayyana cewa yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin a Jihar nan abin ya bawa ne.

Sakataren Kungiyar na Kasa Comrade Sale Birniwa, ya ce kafa kwamatin sasanta yayan Jam’iyar, shine abinda ya kamata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: